Gwamnan Yobe ya yi ƙira ga jami’an tsaro da su tsaurara tsaro a watan Ramadan

0
11
Gwamnan Yobe ya yi ƙira ga jami'an tsaro da su tsaurara tsaro a watan Ramadan

Gwamnan Yobe ya yi ƙira ga jami’an tsaro da su tsaurara tsaro a watan Ramadan

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya jagoranci taron majalisar tsaro na jiha a fadar gwamnati da ke Damaturu, a yau Alhamis. An gudanar da taron ne da shugabannin hukumomin tsaro a daf da shigowar watan Azumin Ramadan.

Gwamnan wanda mataimakinsa Alhaji Idi Barde Gubana ya wakilta ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro a jihar. An bayyana hakan ne yayin taron tsaro da aka saba gudanarwa a jihar. Ya kuma bayyana cewa taron na tsaro ya zama wajibi a duba tare da yin nazari a kan al’amuran tsaro a faɗin jihar tare da tabbatar da ganin ‘yan jihar Yobe sun gudanar da kwanaki 30 na watan Azumin Ramadan lafiya tare da kare dukiyoyinsu yadda ya kamata.

A cewarsa Ramadan yana zuwa da ayyuka da dama da suka haɗa da wa’azi, tarurrukan ƙarawa juna sani, sallar jam’i, buɗa baki da Ƙiyamul Layli, duk wannan yana buƙatar kasancewar jami’an tsaro.

Ya ci gaba da bayyana cewa, a bisa ƙa’ida a lokacin wasu ɓata gari suke aikata munanan abubuwa, akan mutane da duniyoyinsu.

KU KUMA KARANTA:Mummunan hatsarin mota a Yobe, ya kashe mutane 10, uku sun jikkata

Taron ya kuma yaba da ƙoƙarin sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma na magance rikice-rikice a yankunansu.

Mataimakin ya yi amfani da kafafen yaɗa labarai tare da yin ƙira ga malamai masu wa’azin addinin musulunci da su kasance masu jagoranci a karkashin tsari da ƙa’idojin kwamitin da’awa domin bunƙasa rayuwar abin koyi na Manzon Allah (SAW).

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, Ahmad Garba wanda ya samu wakilcin DCP Abdul Abubakar Ozo, ya yi ƙira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya tare da bayar da bayanan da suka dace domin ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.

Sauran shugabannin hukumomin tsaro da suka halarci taron sun haɗa da kwamandan sashin 2 na Operation Lafiya Dole, kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, daraktan tsaro kwamandan tsaro da NSCDC, Kwanturola na Immigration, Kwamandan FRSC da daraktan majalisar zartarwa na ofishin gwamnan kan tsaro.

Leave a Reply