Gwamnan Kano nake son zama, ba shugaban jam’iyyar APC ba – Abdullahi Abbas

0
12
Gwamnan Kano nake son zama, ba shugaban jam'iyyar APC ba - Abdullahi Abbas

Gwamnan Kano nake son zama, ba shugaban jam’iyyar APC ba – Abdullahi Abbas

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya ce shi burinsa ya zama gwamnan Kano ba sake zama shugaban jam’iyyar APC ba a jihar ta Kano.

Abdullahi Abbas ya shaida hakan ne yayin mayar da martani ga ministan ma’aikatar gidaje na Najeriya, Hon Yusuf Abdullahi Ata kan kalamansa na baya-baya nan inda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar.

Ministan ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddun aka sake zaɓen shugaban jam’iyyar na Kano, Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar a karo na hudu.

A yanzu haka zafafan kalaman ministan a wani bidiyo sun karaɗe shafukan sada zumunta, wanda wani abu ne da ke ci gaba da tayar da ƙura a siyasar jihar Kano.

KU KUMA KARANTA:Fitaccen ɗan siyasa a Kano, Alhaji Ahmadu Zago ya rasu

Sai dai shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya shaida cewa Yusuf Ata ‘ba dan jam’iyyar ba ne’ sannan sun yi mamakin dalilan da suka sa aka dauko shi har aka ba shi mukamin minista

”Mu a wajenmu ‘yan jam’iyya, dama ban dan jam’iyya bane, a Kano gaba daya a karamar hukumarsa ne mu ka yi na uku ”

”Kuma ba mu sani ba aka bashi minista kuma har shugaban kasa mu gaya wa cewa ba dan jam’iyyarmu bane, anti party ya yi muna ” in ji shi.

Abdullahi Abbas ya ce sun yi mamakin mukamin minista da shugaba kasa ya ba shi

” Muna mamakin yadda aka yi wannan abun wallahi, dan siyasa ne na karamar hukuma kawai”

Leave a Reply