Majalisar Malamai ta jihar Kano ta yanke hukunci kan rikicin masallacin Bin Uthman da ke Kundila

0
259
Majalisar Malamai ta jihar Kano ta yanke hukunci kan rikicin masallacin Bin Uthman da ke Kundila

Majalisar Malamai ta jihar Kano ta yanke hukunci kan rikicin masallacin Bin Uthman da ke Kundila

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Shugaban majalisar malamai ta Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa bayan zama da dukkanin ɓangarorin da danbarwar sabon masallacin Sahaba da ke Kundila, majalisar ta yanke hukuncin na ƙarshe a kan dambarwar.

” Mun yanke hukuncin Sheikh Muhammad Bn Othman zai koma masallacinsa na Sahaba , shi kuma mai kifi da sauran mutanensa za su cigaba da rike na su masallacin na jami’urrahman”.

KU KUMA KARANTA:‘Yan kasuwa a Kano sun koka kan tsadar Burodi duk da sauƙar farashin fulawa

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana sakamakon zaman da suka yi ga manema labarai a Kano.
Ya ce Sheikh Muhammad Bn Othman ya Amince zai cigaba da jagorantar sallah a tsohon masallacinsa na Sahaba dake kundila, yayin da su kuma su mai kifi za su cigaba da gudanar da harkokin masallacinsu na jami’urrahman.

Leave a Reply