Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ta dakatar da wani fim, ta gayyaci daraktan fim ɗin ofishinta

0
31
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ta dakatar da wani fim, ta gayyaci daraktan fim ɗin ofishinta

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ta dakatar da wani fim, ta gayyaci daraktan fim ɗin ofishinta

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar tace fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta dakatar da wani fim tare da gayyatar dukkannin waɗanda suka fito a cikinsa domin jin ba’asi biyo bayan zargin da akai mata kan mashirya shirin da yin amfani da Kalmar baɗala a matsayin sunan fim ɗin.

Biyo bayan korafin da Hukumar ta karba daga wasu yan kishin Jahar Kano akan wannan film din, Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya bayyana damuwarsa akan alamurin tare da dakatar da film din haka kuma, Abba El-mustapha ya gayyaci dukkannin wanda suka fito a shirin domin jin ba’asi na yin amfani da ita wannan kalma.

KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin fim ko waƙa

Film din mai suna “Zarmalulu” ana zarginsa da rashin ma’ana tare da kama da wani suna na badala a saboda da haka Hukumar ta dakatar da shi tare da kira ga dukkannin wanda suka fito a cikinsa dasu bayyana a gaban kwamatin da Hukumar ta kafa wanda kin yin hakan ka iya jawowa mutum fushin Hukumar.

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano na da hurumin kan dakatar da dukkannin wani film da bata gamsu da yadda aka shiryashi ba tare da laddaftar da duk wani da tasamu da yin abinda bai kamata a cikin kowanne film ba ko kuma a wajen film din matsawar dan Masana’antar kannywood ne.

Leave a Reply