Za mu yi bincike kan kisan da aka yi wa mutane a Rimin Zakara – Gwamnatin Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da bincike na musamman dan gano musabbabin rikicin da ya faru a unguwar Rimin zakara wanda yai sanadiyyar rasa rayukan mutane.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai kan rikicin da aka samu tsakanin jami’an tsaro da mutanan dake zaune a yankin.
Waiya ya kuma ce Jami’ar Bayero ce ta nemi taimakon gwamnatin Kano dan a dawo mata da filayenta, wanda hakan ya sa ta shiga tsakani kuma aka baiwa mutanan da ke zaune a gurin wa’adin tashi kasancewar lokacin da aka basu ya riga ya kare.
KU KUMA KARANTA:An harbe mutane 4 a rikicin da ya ɓarke tsakanin jama’a da jami’an tsaro kan rusau a Kano
Daga nan waiya yace bata gari ne su ka shiga cikin lamarin domin tada zaune tsaye duk kuwa da jami’an tsaron da wadancen mutanen su ka gayyato gudun tada fitina.
Kwamred Waiya yace, lallai Gwamnatin Kano zata kafa kwamitin da zai gudanar da bincike Kan Wanda suka haddasa rikicin da yayi sanadiyyar rayukan Mutane uku.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito al’ummar unguwar Rimin zakara a jiya litinin sun zargi ma’aikatar Kasa ta Kano da rushe musu gidajensu da hadin kan jami’ar Bayero, lamarin da ya jawo har jami’an tsaro suka kashe mutane 4 tare da jikka wasu 16 .









