Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda 358 tare da kama wasu 431
Rundunar sojin Najeriya tace dakarunta sun hallaka ‘yan ta’adda 358 tare da kama 431 a watan Janairun da muke ciki.
Daraktan yada labaran ma’aikatar tsaron najeriya, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a yau Juma’a, yace hakan ci gaba ne a kan yunkurin da rundunar ke da shi na samun galaba a kan ‘yan ta’addar da abokan burminsu a aikin da ake gudanarwa na kakkabe masu tada kayar baya da ‘yan ta’adda a fadin kasar.
KU KUMA KARANTA:Sojojin Najeriya sun kashe mataimakin Turji da wasu mayaƙansa da dama
Ya kara da cewa dakarun sun kuma kama barayin danyen man fetur 59 tare da kubutar da mutane 249 da masu garkuwa da mutane ke rike dasu.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, a shiyar kudu maso kudu, dakarun sun musunta batun satar man da aka kiyasta kudinsa ya zarta naira biliyan 2.