Gwamnatin Kano za ta kashe Naira biliyan 2 a auren Zauwarawa

0
8
Gwamnatin Kano za ta kashe Naira biliyan 2 a auren Zauwarawa

Gwamnatin Kano za ta kashe Naira biliyan 2 a auren Zauwarawa

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin jahar Kano ta ware Naira biliyan 2.5 domin gudanar da auren zaurawa daga kananan hukumomi 44 na jihar a shekarar 2025.

Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kudi na Jihar, Musa Shanono, ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ‘yan jarida bayani kan yadda kasafin kudin shekarar 2025 da Majalisar Dokokin Jihar ta amince da shi ya kasu.

KU KUMA KARANTA:Kwankwaso da Abba sun jagoranci aurar da zaurawa 1,800 a Kano

Ya kara da cewa daga cikin adadin kudin, an ware Naira biliyan 1 don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan.

Ya kuma ce Naira miliyan 955 an ware ta ne don gudanar da binciken kididdigar ma’aikata, binciken halin da gidaje ke ciki da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Bugu da kari, ya bayyana cewa an ware Naira miliyan 267.6 don samar da kayayyakin more rayuwa da kuma tallafa wa shirye-shiryen Da’awah na addinin Musulunci.

Leave a Reply