Gwamna Kano ya jinjinawa rundunar ‘yansanda kan tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano

0
40
Gwamna Kano ya jinjinawa rundunar 'yansanda kan tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano

Gwamna Kano ya jinjinawa rundunar ‘yansanda kan tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano

Daga Idris Umar, Zariya

Abba Kabir Yusuf, ya yabawa rundunar ƴansandan jihar bisa rawar da take takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake mora a jihar.

Abba ya yi wannan yabo ne yayin da ya ke karɓar bakuncin matar Sufeto Janar na ‘yansanda, Misis Elizabeth Egbetokun, wadda ta kai masa ziyara ta musamman a gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin.

Gwamnan ya bayyana cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a Kano ya samu ne saboda jajircewa da ƙwarin gwiwar rundunar ‘yansandan jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sanda, Salman Dogo Garba.

KU KUMA KARANTA:Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu, kwana 1 da rantsar da shi

“Kano ba ta taɓa samun irin wannan ba, saboda yanzu muna da ƴansanda jajirtattu inda kwamishinan ‘yan sanda da AIG na shiyya ta daya ke aiki tukuru sansu don samar da zaman lafiya,” inji gwamnan.

Har ila yau, ya yaba wa matar Egbetokun saboda kyawawan halayenta, jajircewarta, da ƙaunarta ga matan ‘yansanda.

Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ‘yansanda da kayan aiki domin su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ba reshen kungiyar matan jami’an ‘yan sanda (POWA) na jihar Kano fili tare da tallafin kuɗi domin gina ofishinsu na gudanar da harkokinsu.

Leave a Reply