Aƙalla mutum 100 sun mutu a wata mahaƙar gwal ba bisa ƙa’ida
Mutum aƙalla 100 sun mutu a wata mahaƙar gwal ba bisa ƙa’ida ba a Afirka ta Kudu.
Ana zargi mutanen maza sun mutu ne sakamakon yunwa da galabaita bayan sun kwashe watanni a ƙarƙashin mahaƙar ma’adinan a yayin da ‘yan sanda suka yi yunƙurin korarsu daga ciki, a cewar wasu wakilai na mutanen.
Ranar Litinin wakilan masu haƙar ma’adinan sun ce har yanzu akwai fiye da mutum 500 da ke ƙarƙashin mahaƙar ma’adinan.
Sabelo Mnguni, wani mai magana da yawun ƙungiyar mahaƙa ma’adinai mai suna Mining Affected Communities United in Action Group, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press wasu bidiyoyi biyu da aka ɗauka da wayar salula sannan wasu daga cikin waɗanda suka tsira suka fito da ita ranar Juma’a sun nuna gomman gawawwaki da aka naɗe da ledoji.
KU KUMA KARANTA: Za mu ɗauki matakan gaggawa don ceto rayukan masu haƙar maadinai; Shugaba Ramaphosa
Mnguni ya ce “aƙalla” mutum 100 maza sun mutu a mahaƙar ma’adinan da ke lardin North West, inda ‘yan sanda suka soma ƙaddamar da aikin korar masu haƙar ma’adinan a watan Nuwamba.
Mnguni ya ƙara da cewa ana zargin yunwa da galabaita ne suka yi sanadin mutuwar mutanen. Ya ce an fito da gawawwaki 18 ranar Juma’a.