‘Yan kwana-kwana na ci gaba da yaƙi da gobarar daji mafi girma a Amurka

0
7
'Yan kwana-kwana na ci gaba da yaƙi da gobarar daji mafi girma a Amurka

‘Yan kwana-kwana na ci gaba da yaƙi da gobarar daji mafi girma a Amurka

Jami’an kashe gobara a birnin Los Angeles sun yi fama da harsunan wuta a rana ta hudu a jere a jiya Juma’a, inda suke kokarin shawo kan gobarar daji da ta lalata dubban gidaje tare da kashe akalla mutane 10.

Jami’ai sun yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu, wanda aka sabunta shi a yammacin ranar Alhamis, na iya karuwa, idan aka sami shawo kan gobarar mai dimbin harsuna daban-daban, inda ma’aikata za su iya karade wurin da ta mamaye.

KU KUMA KARANTA:Hukumar DSS ta kama shugaban NLC, Ajaero

An ci gaba da aikin kashe gobarar a cikin dare har zuwa safiyar jiya Juma’a, inda jirage masu saukar ungulu masu zuba ruwa suka yi amfani da damar da aka samu ta wucin gadi a yanayin iska.

Shugaban Amurka Joe Biden ya kira manyan jami’ai a jiya Juma’a, domin tattaunawa kan matakin da gwamnatin tarayya za ta dauka kan gobarar dajin.

Ya zuwa safiyar jiya Juma’a, an sami damar dakile kashi 8 kacal cikin 100 na gobarar ta Palisades wadda ita ce mafi girma, a cewar ma’aikatar gandun daji da Kare Gobara ta California. Gobarar ta kone fili sama da hekta 8,000.

Leave a Reply