Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu, kwana 1 da rantsar da shi

0
41
Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara, ya rasu kwana 1 da rantsar da shi

Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu, kwana 1 da rantsar da shi

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan aiyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure ya rasu, kwana ɗaya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da shi a gidan gwamnati.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, marigayin ya rasu a yau Laraba a ƙasar Egypt.

Ya ce Gwamna Yusuf, wanda ya nuna kaɗuwa ga rasuwar Bunkure, ya baiyana mutuwar ta sa matsayin babban rashi ga iyalinsa da ma Kano baki ɗaya.

“Wannan wani yanayi ne na kaɗuwa da alhini saboda Injiniya Bunkure mutum ne mai hazaƙa da sanin makamar aiki wanda jihar Kano za ta amfani da shi.

KU KUMA KARANTA: Rashin Ruwan Sha: Alummar garin Kanwa da ke Kano suna shan ruwan da dabbobi ke sha

” Allah Ya gafarta masa Ya baiwa iyalin sa da mu baki ɗaya hakurin rashin sa,” in ji Gwamnan.

Leave a Reply