Yadda NNPC ta yi fatali da tayin Ɗangote na dala miliyan 750 domin gudanar da matatun man Najeriya – Obasanjo

0
23
Yadda NNPC ta yi fatali da tayin Ɗangote na dala miliyan 750 domin gudanar da matatun man Najeriya - Obasanjo

Yadda NNPC ta yi fatali da tayin Ɗangote na dala miliyan 750 domin gudanar da matatun man Najeriya – Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda kamfanin man fetur din Najeriya (NNPC) ya yi fatali da tayin dala miliyan 750 da hamshakin dan kasuwar nan Aliko Dangote ya yi a 2007 domin gudanar da matatun man Fatakwal da Kaduna.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wata kebabbiyar hira da tashar talabijin ta Channels.

Ya kara da cewa NNPC, da yanzu aka sauyawa fasali zuwa NNPCL, ya san cewa ba shi da karfin da zai iya gudanar da matatun man Najeriya amma duk da hakan yayi fatali da tayin na dangote.

KU KUMA KARANTA:Zaɓen 2027: Ba mu cimma yarjejeniyar haɗewa da PDP, NNPP ba – Peter Obi

A cewar Obasanjo, “Aliko ya hado tawaga sannan suka biya dala milyan 750 domin shiga kawance tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa (PPP) da zai gudanar da matatun man. shugaban daya gaje ni ya mayar musu da kudinsu don haka naje na same shi na shaida masa abinda ya faru. Ya shaida mini cewar nnpc yace yana bukatar matatun kuma zai iya gudanar dasu. nan take nace masa kasan ba zasu iya gudanar dasu ba.”

Obasanjo ya kasance zabebban shugaban najeriya tsakanin watan Mayun 1999 da Mayun 2007. kuma ya kasance shugaban mulkin sojan kasar tsakanin watan Febrairun 1976 da Oktoban 1979.

Leave a Reply