Jami’an tsaro sun kama ‘yan tawayen Kamaru a Taraba
Dakarun Burged ta 6 na rundunar sojin Najeriya dake shiya 3, masu aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Whirl Stroke, sun kama mambobi 4 na ƙungiyar ‘yan tawayen Ambazonia daga jamhuriyar a Kamaru a jihar Taraba.
An kama mambobin ƙungiyar da ake zargin ‘yan tawayen Ambazonia ne a wani otel dake ƙaramar hukumar Takum ta jihar.
Sakamakon samun sahihan bayanan sirri a rana r 18 ga watan Disamban da muke ciki, dakarun sun bi diddigi tare da damƙe mutanen.
A sanarwar daya fitar, mai riƙon muƙamin muƙaddashin darakta kuma kakakin burged ta 6 ta rundunar sojin Najeriya, Olubodunde Oni, yayin binciken farko yace, waɗanda ake zargin sun yi iƙirarin cewar su wani ɓangare ne na ƙungiyar ‘yan tawayen dake da hannu a safarar makamai ta hanyar musayar ‘ya’yan coccoa da abokan haɗin bakinsu dake Najeriya.
KU KUMA KARANTA: Jami;an tsaro sun tarwatsa sansanin Lakurawa a Sokoto da Kebbi
An ƙwato wayoyin hannu guda 4 mutanen da ake zargin waɗanda suke tsare a yayin da ake cigaba da bincike.