Najeriya ta ci kyautuka 3 a bikin ba da lambobin yabo na ƙwallon ƙafa a Afirka

0
24
Najeriya ta ci kyautuka 3 a bikin ba da lambobin yabo na ƙwallon ƙafa a Afirka

Najeriya ta ci kyautuka 3 a bikin ba da lambobin yabo na ƙwallon ƙafa a Afirka

‘Yan wasan Najeriya maza da mata sun lashe kyautuka a rukunoni uku na ƙwallon ƙafar Afirka na hukumar CAF. Ga yadda ta kaya a rukunoni daban-daban na bikin da ya gudana a Morocco.

Gwarzon ɗan wasan Afirka: Ademola Lookman
Wanda ya lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Afirka, Ademola Lookman, dan wasan gaba ne na tawagar Najeriya, wanda ya taka rawar gani a gasar AFCON da Najeriya ta zo ta biyu a farkon shekarar nan.

Lookman ya kafa tarihin cin ƙwallaye uku rigis a wasan ƙarshe na gasar Europa da ƙungiyar da yake buga wasa ta Atalanta ta Italiya ta lashe, bayan doke Bayer Leverkusen da ci 3-0.

Gwarzuwar ‘yar wasan Afirka
Barbra Banda ‘yar Zambia ce ta gwarzuwar ‘yar ƙwallon ƙafa rukunin mata a Afirka ta CAF a shekarar 2024. Barbra Banda mai shekaru 24 ‘yar wasan gaba ce kuma kyaftin ɗin tawagar ƙasar Zambia.

Gwarzuwar tawaga
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Ivory Coast ce gwarzuwar tawagar ƙasa a rukunin maza a bana. Tawagar ce dai ta lashe kofin ƙasashen Afirka na AFCON 2023 da aka yi a watan Janairun shekaran nan a can Ivory Coast ɗin.

Kamar a bara, tawagar Super Falcons ta Najeriya ce ta lashe kyautar gwarzuwar tawagar ƙasa ta mata a shekarar 2024, bayan doke tawagogin Morocco da Afrika ta Kudu.

KU KUMA KARANTA: Ademola Lookman na kan gaba wajen lashe kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa na Afrika ta bana

Gwarazan koci
Kocin tawagar Ivory Coast ta maza, Emerse Fae shi ne gwarzon kocin Afirka na bana. Fae ya fara gasar AFCON ta bana a matsayin mataimakin koci Jean-Louis Gasset wanda ya yi murabus ya bar Fae wanda shi ya kai tawagar zuwa lashe kofin.
Lamia Boumehdi ce ta lashe kyautar gwarzuwar koci rukunin mata a Afirka a 2024. Lamia ‘yar asalin Morocco ce, kuma ita ta jagoranci TP Mazembe wajen lashe kofin zakarun nahiyar Afirka na mata, bayan lashe kofin mata na Congo DR.

Gwarzuwar ƙungiya
Al Ahly ta Masar ce gwarzuwar ƙungiyar ƙwallo a nahiyar Afirka a 2024, inda ta lashe kyautar a karo na uku a jere a bana, yayin da ƙungiyar TP Mazembe ta zama gwarzuwar ƙungiyar mata ta Afirka a bana.

Gwarazan masu tsaron gida
Gwarzon mai tsaron gida na Afirka rukunin maza shi ne Ronwen Williams, ɗan asalin Afirka ta Kudu, wanda ke tsaron gidan tawagar maza ta Afirka ta Kudu.

Chiamaka Nnadozie ta Najeriya ce ta lashe gwarzuwar mai tsaron gida ta Afirka rukunin mata.

Mai shekaru 24, Chiamaka haifaffiyar jihar Imo ce a kudu maso gabashin Najeriya, kuma tana buga wa tawagar mata ta Najeriya da kuma ƙungiyar Paris FC a matsayin mai tsaron gida.

Matasan ‘yan wasa
Gwarzon ɗan wasan Afirka a bana shi ne Lamine Camara, ɗan Senegal da ke buga wa AS Monaco a Italiya. Camara ɗan wasan tsakiya ne mai shekaru 20 da yake buga wa tawagar ƙasar Senegal.

A rukunin mata, Doha El Madani ‘yar asalin Morocco ce ta lashe kyautar gwarzuwar matashiyar ‘yar ƙwallo, saboda ƙoƙarinta a gasar zakarun nahiyar Afirka ta CAF.

Leave a Reply