Farmaƙin Isara’ila ta sama ya kashe aƙalla mutane 18 a Gaza.

0
23
Farmaƙin Isara'ila ta sama ya kashe aƙalla mutane 18 a Gaza.

Farmaƙin Isara’ila ta sama ya kashe aƙalla mutane 18 a Gaza.

Ma’aikatan lafiya sun ce a wani harin saman kuma, kimanin mutane 10 ne aka kashe a daura da ofishin yankin dake Deir-Al-Balah a tsakiyar zirrin Gaza inda mutane suka taru don karban tallafin jinkai.

Akalla Falasdinawa 18 ne aka kashe a wani farmakin saman Isra’ila a yau Asabar a Gaza, a cewar ma’aikatan lafiya, yayin da sojojin Isra’ila suka ce sun auna wani dan Hamas dake samun mafaka a matsugunan mutane da wuraren adana kayan tallafin jinkai.

KU KUMA KARANTA:FBI ta Amurka, ta cafke wani ɗan Najeriya kan zargin damfarar dala miliyan 6 ta Intanet

An kwashe wadanda harin ya rutsa da su a kafa, sahu-sahu da motocin mutanen daga inda aka kai harin, inji ma’aikatan lafiyar. Harin ya kashe shugaban kwamitin gudanarwa na Hamas a tsakiyar Gaza, a cewar wata majiyar Hamas.

A wani farmaki a wani ginin da a baya ake amfani da shi a matsayin matsugunin mutanen da suka rasa gidajen su a birnin Gaza kuma Akalla mutane 7 ne aka kashe a cewar ma’aikatan lafiyar Falasdinu, har da wata mata da jaririn ta.

Leave a Reply