Najeriya za ta ci gajiyar tsarin tattalin arzikin Hydrogen – Ƙaramin Ministan man fetur

0
14
Najeriya za ta ci gajiyar tsarin tattalin arzikin Hydrogen - Ƙaramin Ministan man fetur

Najeriya za ta ci gajiyar tsarin tattalin arzikin Hydrogen – Ƙaramin Ministan man fetur

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ta fara shirye-shiryen yadda ƙasar za ta amfana da tsarin tattalin arzikin sinadarin iskar hydrogen na duniya da ake hasashen zai ci gaba da habaka zuwa fiye da dala biliyan 200 kan nan da shekarar 2030.

A jawabinsa yayin taron tattalin arzikin hydrogen na farko a Abuja a ranar Talata, ƙaramin ministan albarkatun man fetur (ɓangaren iskar gas), Ekperikpe Ekpo yace iskar gas ɗin da ake samarwa yayin amfani da makamashin da ake iya sabuntawa zai samarda wata dama ta musamman da zata cike gibin buƙatar Najeriya ta makamashi.

A cewarsa, batun iskar hydrogen a Najeriya a bayyane yake, kasancewa Allah ya albarkaci ƙasar da dimbin albarkatun da za a iya sabuntawa, daga hasken rana dake yankin arewaci zuwa iskar dake yankunan gabar tekun dake kudu.

Ministan ya ƙara da cewar wurin da Allah ya ajiye Najeriya ya bata kyakkyawar damar cin kasuwannin nahiyoyin Turai da Afirka, inda yace za a iya yin amfani da bututun iskar gas din da ake da shi yanzu wajen yin safarar hydrogen ɗin.

KU KUMA KARANTA: Kamfanin NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur

A nasa jawabin shima, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, wanda ya samu wakilcin hadimin shugaban ƙasa na musamman akan lantarki da kayayyakin more rayuwa, Sadiq Wanka, yace Najeriya zata juya akalarta ga iskar hydrogen wajen biyan buƙatunta na makamashi, inda yace domin cimma wannan katafaren buri, yana da matuƙar muhimmanci a gina kwakkwaran layin samar da lantarki ta mabambantan makamashi.

Leave a Reply