Matatar mai na Ɗangote ya rage farashin fetur ɗinsa

0
15
Matatar mai na Ɗangote ya rage farashin fetur ɗinsa

Matatar mai na Ɗangote ya rage farashin fetur ɗinsa

Kamfanin mai na Ɗangote ya sanar da rage farashin fetur ɗinsa da yake sayar wa ‘yan kasuwa zuwa N970 daga N990.

Shugaban sashen watsa labarai na kamfanin Anthony Chiejina ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa an rage farashin ne domin “yaba wa mutanen Najeriya”.

“A daidai lokacin da ƙarshen shekara ke ƙaratowa, wannan ce hanyarmu ta yaba wa jama’ar Najeriya dangane da irin goyon bayan da suka bayar domin tabbatar da wannan matatar man ta samu.

Bugu da ƙari, muna gode wa gwamnati dangane da irin goyon bayanta domin hakan zai ƙara bisa matakan da aka ɗauka don karfafa sana’o’in cikin gida don kyautata rayuwar jama’a,” in ji sanarwar.

Ɗangoten ya ce zai ci gaba da samar da man fetur mai kyau ga ‘yan Najeriya ba tare da rage masa inganci ba.

KU KUMA KARANTA: Kamfanin NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur

A farkon watan nan ne matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa ta fara sayar da fetur a kan naira 990 kan kowace lita da za a loda a tankar dakon mai ko kuma naira 960 kan kowace lita ga jiragen ruwa.

Hakan ya biyo bayan rashin jituwar da aka rinƙa samu tsakanin kamfanin Dangote da kuma NNPCL dangane da abubuwa da dama waɗanda suka shafi jigilar man fetur da farashin man fetur da sauransu.

Haka kuma an ta samun kwan-gaba-kwan-baya tsakanin kamfanin na Dangote da kuma ‘yan kasuwa masu dakon man fetur dangane da yadda za su sayi mai da kuma dakonsa.

Leave a Reply