Gwamnan Ekiti ya amince da biyan ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

0
25
Gwamnan Ekiti ya amince da biyan ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan Ekiti ya amince da biyan ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnatin jihar Ekiti ta amince da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikata a jihar.

Amincewar ta biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago, wacce ta bayyana cewa, sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.

Shugabar ma’aikata, Dr. Folakemi Olomojobi ce ta sanya hannu a madadin gwamnatin jihar kan yarjejeniyar, yayin da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a jihar suka sanya hannu a madadin ma’aikata.

Shugabar ma’aikatan ta ce, Gwamna Biodun Oyebanji ya amince da tsarin biyan sabon mafi karancin albashin yadda kwamitin mafi karancin albashi ya gabatar da shi don ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta amince da biyan ₦71,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi 

Da take bayyana Gwamna Oyebanji a matsayin “gwamna abokin ma’aikata” wanda ke fatan alheri ga ma’aikata a jihar, Dokta Olomojobi ta yi amfani da wannan dama wajen bayyana godiyarta ga shugabannin kwadago bisa fahimtarsu, haƙuri da jajircewarsu wajen ganin sun cimma nasara ga ma’aikata.

Ta kuma gode wa ma’aikatan Ekiti bisa haƙurin da suka nuna kan sakamakon hukuncin da kwamitin ya yanke da kuma yadda suka amince da gwamnatin jihar.

Leave a Reply