Mun ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi domin ragargazar ’yan ta’adda – Ministan Tsaro

0
70
Mun ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi domin ragargazar ’yan ta'adda - Ministan Tsaro

Mun ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi domin ragargazar ’yan ta’adda – Ministan Tsaro

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce sojoji suna aiki tukuru don murkushe ayyukan Lakurawa da sauran ’yan ta’adda da ke addabar yankin Arewa.

Ministan wanda ya kai ziyarar aiki tare da duba kayayyakin yakin jirage na rundunar Operation Fansan Yamma, a Jihar Sakkwato ranar Litinin, ya ce sojoji sun dauki wani kwakkwaran mataki kan Lakurawa.

Ya ce, “Kun ji daga bakin shugaban ƙaramar hukumar da Lakurawa suka kai wa hari a Jihar Kebbi, yana bayyana yadda sojoji suka mamaye yankin suka fatattaki Lakurawa

“Hakan ya faru ne sakamakon jajircewa da jami’an tsaronmu suke yi,” a cewar ministan tsaron.

KU KUMA KARANTA: Jamian tsaro sun kama;yan bindiga 3 da mai yin safarar makamai

Ya ci gaba da cewa mutanen yankunan da abin ya shafa ne suka fi kowa bakin  da za su yi magana aikin sojoji, domin su ganau ne a kan farmakin da sojoji ke kai wa mayakan.

“Mun kaddamar da wani sabbin makamai a Katsina tare da ƙaddamar da sabbin jiragen yaki masu sauƙar ungulu domin ragargazar ’yan fashin daji da da kuma Lakurawa, kuma za mu sake tura wasunsu zuwa Sakkwato,” in ji ministan.

Ya kai wa sojojin ziyara ne tare da Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Hasan Bala Abubakar da wasu manyan hafsoshin soji.

Leave a Reply