Obasanjo ba shi da kimar sukar gwamnati mai ci – Gwamnatin Tarayya

0
109
Obasanjo ba shi da kimar sukar gwamnati mai ci - Gwamnatin Tarayya 

Obasanjo ba shi da kimar sukar gwamnati mai ci – Gwamnatin Tarayya

Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan caccakar da tsohon shugaban ƙasar Janar Olusegun Obasanjo ya yi wa shugaba mai ci Bola Tinubu dangane da manufofinsa na tattalin arziƙi.

Obasanjo ya caccaki gwamnatin ta shugaba Tinubu ne yayin jawabin da ya gabatar a wani taro kan shugabanci da ya halarta a jami’ar Yale da ke Amurka.

Yayin taron, tsohon shugaban ya ce yanzu haka duk wasu alamu na gazawa ko rushewa daga matsayin ƙasa ya tabbata akan Najeriya, laifin da ya ɗora akan masu madafun ikon da ya bayyana a matsayin masu tsananin son rai, cin hanci da rashawa, rashin ɗa’a da kuma gazawa wajen shugabanci nagari.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ko na biyu da Obasanjo ke caccakar mahukuntan da suka biyo bayan gwamnatin da ya jagoranta ba, musamman ma akan fannin tattalin arziƙi.

Sai dai a nata martanin, fadar gwamnatin Najeriya ta hannun mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan sadarwa, Sunday Dare, ta ce Obasanjo ba shi da kimar sukar gwamnati mai ci, la’akari da irin ɓarnar da yayi a zamanin gwamnatin da ya jagoranta, ta hanyar kassara tsarin dimokaraɗiya.

Cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Sunday Dare ya ce ga dukkanin alamu Obasanjo ya manta da cewar ya daɗe da kafa tarihin zama shugaban da ya jagoranci gwamnatin da matsalar cin hanci da rashawa ta yi wa katutu mafi muni a tarihin Najeriya.

A cewar Dare, a zamanin gwamnatin tsohon shugaban aka ware dala biliyan $16 don samar da wutar lantarki, maƙudan kuɗaɗen da har yanzu babu labarin inda suke, saboda kwanciyar magirbin da aka yi akansu. Dan haka abin dariya ne Obasanjo ya riƙa faɗakarwa akan laifukan cin hanci da rashawa.

KU KUMA KARANTA: Za mu ƙara haɓaka alaƙarmu da sabon zaɓaɓɓen shugaban Amurka – Gwamnatin Tarayya

Sukar da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya yi ta zo ne kusan lokaci guda da shaguɓen da asusun bayar da lamuni na Duniya IMF ya yi kan manufofin tattalin arziƙin shugaba Bola Tinubu.

Cikin sabon rahoton da ya wallafa a kan tattalin arziƙin yankin Kudu da Saharar  Afrika, ausun na IMF ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da har yanzu ta gaza cimma nasarar samun riba daga sauye-sauyen tsarin tattalin arzƙin da take aiwatarwa.

Rahoton na IMF ya ƙara da cewar, a yayin da aka fara darawa da sambarka a wasu ƙasashen yankin Kudu da Saharar, lamarin ya sha bambam a Najeriya, inda har yanzu lamura ke tafiyar Hawainiya.

Mai yiwuwa rahoton na IMF ya bai wa wasu mamaki, la’akari da cewa asusun ba da lamunin ya daɗe yana shan caccaka daga ‘yan Najeriya waɗanda ke zargin shi ne ke bai wa mahukuntan nasu shawarwarin da ba sa ɓullewa, tare da ingiza su wajen aiwatar da tsauraran manufofin tattalin arziƙin da ke jefa marasa ƙarfi cikin ƙunci.

Leave a Reply