Ƙungiyar ACF ta buƙaci sojoji su gaggauta murƙushe sabuwar ƙungiyar ta’addanci, Lakurawa

0
40
Ƙungiyar ACF ta buƙaci sojoji su gaggauta murƙushe sabuwar ƙungiyar ta'addanci, Lakurawa

Ƙungiyar ACF ta buƙaci sojoji su gaggauta murƙushe sabuwar ƙungiyar ta’addanci, Lakurawa

Ƙungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta buƙaci sojojin Najeriya su yi ƙoƙari wajen murƙushe sabuwar ƙungiyar ta’addancin wato Lakurawa wadda ta ɓulla a Sokoto da Kebbi da ke arewacin ƙasar.

Ƙungiyar ta ACF ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labaranta Farfesa Tukur Muhammad Baba.

Ƙungiyar ta buƙaci sojojin ƙasar su yi amfani da duk wasu kayan aikinsu domin tabbatar da cewa sun murƙushe ‘yan ta’addan.

ACF ɗin ta yi gargaɗi kan cewa kada a ɗauki wannan sabuwar ƙungiyar da wasa ko kuma a bar ta cikin al’umma kamar yadda aka yi sakaci da batun Boko Haram da rikicin manoma da makiyaya da ‘yan garkuwa da mutane.

Ƙungiyar ta ACF ta ce ɓullar wannan sabuwar ƙungiyar ta Lakurawa ta jawo buƙatar kafa wata sabuwar rundunar ƙawance ta ƙasa da ƙasa tsakanin Najeriya da makwabta inda ta ce akwai buƙatar a samu haɗin kan Jamhuriyar Nijar wajen sanya kanta a ciki.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin sojojin Chadi da kashe ɗimbim masunta a Najeriya

“Akwai buƙatar a yi amfani da ziyarar da babban hafsan tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa ya kai Jamhuriyar Nijar a farkon wannan shekarar a matsayin wata dama don ƙoƙarin da ake yi na ƙasa da ƙasa domin murƙushe ta’addanci,” in ji sanarwar.

A makon da ya gabata ne dai Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da ɓullar ƙungiyar Lakurawa a yankin Sokoto da Kebbi.

Leave a Reply