Aƙalla mutane 12 sun mutu a wani zaftarewar ƙasa
Ma’aikatan bayar da agaji sun gano gawawwaki 12 sakamakon wata zaftarewar ƙasa da ta faru a yammacin Kamaru, kamar yadda wani jami’in yanki ya bayyana a ranar Asabar, inda ya ƙara da cewa babu tabbacin gano wasu masu rai.
Kafar watsa labarai ta ƙasar CRTV ta ruwaito gwamnan yankin Ouest, Augustine Awa Fonka, yana tofa albarkacin bakinsa dangane da lamarin.
“A ganinmu, ba mu tunanin akwai yiwuwar a sake gano wani mai rai,” kamar yadda ya shaida wa kafar watsa labaran.
An gano gawawwaki 12 daga wurin da lamarin ya faru, mutum na ƙarshe shi ne a ranar Asabar, in ji shi.
Har yanzu akwai gomman mutane da ba a gansu ba, inda ake ci gaba da neman gawawwakinsu, kamar yadda ya ƙara da cewa.
KU KUMA KARANTA: Zaftarewar ƙasa ta yi ajalin aƙalla mutum 157
Zaftarewar ƙasa biyu ta faru a saman wani tsauni a ranar Talata – ta biyun a daidai lokacin da ma’aikatan bayar da agaji ke amfani da manyan kayayyakin aiki domin gyara hanya.
Ƙasar ta zaftare da manyan motoci uku masu ɗaukar mutum 20, da motoci masu ɗaukar mutum biyar da babura da dama, kamar yadda Awa Fonka ya bayyana a sanarwarsa ta baya.
Hanyoyin ƙasar Kamaru suna da hatsarin gaske, inda kusan mutane 3,000 ke mutuwa a kowace shekara a sanadiyyar hadurra, ko kuma sama da mutum 10 daga cikin mazaunan 100,000, a cewar sabbin alkalumman Hukumar Lafiya ta Duniya, da aka buga a shekarar 2023.