Takardar Naira 100 ta fara ƙaranci a cikin al’umma

0
36
Takardar Naira 100 ta fara ƙaranci a cikin al'umma

Takardar Naira 100 ta fara ƙaranci a cikin al’umma

Daga Idris Umar, Zariya

Masu ƙananan sana’o’i sun fara kokawa kan ƙarancin takardar kuɗi ta Naira 100 wanda ke kawo musu tsaiko a harkokin kasuwancinsu a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Mutane daban-daban kamar ‘yan kasuwa da masu tuƙa ababen hawa na haya masu sana’ar POS sun koka sosai yayin da suke zantawa da wakilinmu musamman yadda ƙarancin takardar Naira 100 ke shafar kasuwancinsu a kowace rana wanda hakan yasa kasuwar tasu na neman durkushewa baki ɗaya.

Wasu daga cikin mutanen da suka zanta da wakilin namu sun baiyana cewa wa irin halin da suke ciki sun zargi bankuna da riƙe kuɗin inda wasu kuma ke ganin cewa laifin babban bankin Najeriya kai tsaye bisa rage buga kuɗin a wadace.

Sai dai har yanzu babban bankin Najeriya bai ce komai ba game da zargin da ake mashi.

Bincike ya tabbatar da cewa al’amari dai ya bar ƙasar nan cikin ruɗani kan matsalar ƙarancin kuɗin.

Wanda hakan yana taimakawa durkushewar jari ga masu ƙaramin karfi.

Wasu ‘yan Najeriya ke cewa rashin wadatar takardar kuɗin na da alaƙa da tashin gwauron zabin kayayyaki wanda ke ƙara sa mutane neman takardar kuɗin.

KU KUMA KARANTA: Wani mutum ya kashe ɗan uwansa a dalilin naira 1500 kudin wutar lantarki, a jihar Anambra

Ƙididdigar tashin farashin kaya a Najeriya ya kai kaso 32.7% a watan Satumba wanda hakan ya ƙara sa farashi kayayyaki tashi fiye da kima da kuma buƙatar ƙananun kuɗi.

A wasu wurare kamar rukunin gidaje na ACO da ke Abuja da ke kan titin zuwa filin jirgin sama, suna fama da matsalar karancin takardun kuɗi saboda yawan amfani da takardun kuɗi.

Sayyada uwa ce da ‘ya’ya biyar da ke sayar da tumatur kusa da ofishin ‘yan sanda kusa da wata babbar kasuwa, ta nuna damuwarta kan yadda ƙarancin Naira 100 inda ta ce akwai wasu ranakun ma da take zuwa kasuwar ta dawo ba tare da riƙe takardar kuɗin ba.

Duk da kasuwancinta bai dogara da cinikin Naira 100 ba, amma akwai lokutan da za a buƙaci canji. Wannan ya jawo mata asarar ciniki inda a wasu lokutan sai dai ta ba wa masu siyayyar attarugu a maimakon canjin.

‘Yan kasuwa kamar Agnes James, wadda ke sana’ar sayar da abinci a kasuwar, ta ce wannan rashin Naira 100 ya tilasta mata koyon dabarun kamar ƙananun alawowi domin bai wa kwastamominta a maimakon canjin.

“Na rasa ciniki sosai saboda rashin takardun kuɗin nan kuma ka san sana’ar babu wata ribar sosai. Akwai lokacin da zan cewa kwastamomi ku san 10 su tafi saboda babu canji, wasu sukan dawo su ba ni, wasu kuma sun tafi kenan,” in ji matar.

Shi ma wani ma’aikacin Kamfani mai suna Adamu Magaji wanda ke shiga motar haya domin zuwa wurin aikinsa, ya ce sau tari da yawa sai dai ya fi biya ƙarin kuɗin mota sama da yadda ya kamata ya biya saboda idan misali ya ba da N1000 a inda kuma zai biya N900 ya kamata ya biya, to masu motar ko babur kan ce sai dai kawai su biya 1000 ɗin kuma mutum ba shi da zaɓi dole hakan zai biya

Bisa haka ne wata malama mai sana’ar sayar da biredi tayi ƙira ga dukkan wanɗanda suke da hakkin magance wannan lamarin su yi wa Allah su gyara lamarin don taimakawa ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply