Burkina Faso ta kori wasu sojoji 14 daga aiki

0
47
Burkina Faso ta kori wasu sojoji 14 daga aiki

Burkina Faso ta kori wasu sojoji 14 daga aiki

Ofishin shugaban ƙasar Burkina Faso Ƙyaptin Ibrahim Traore ya sanar da korar wasu tarin sojoji daga aikin soja, ciki kuwa har da tsohon shugaban juyin mulkin ƙasar Laftanar Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba.

Bayanai sun ce an cirewa mutanen 14 rigar soja ne bayan zargin su da cin zarafin aikin soja, da kuma zubar masa da mutunci a idanun duniya.

Cikin manyan zarge-zargen da ake yiwa mutanen har da haɗa kai da manyan ƙasashen duniya da basa ga maciji da ƙasar da kuma ƴan ta’adda, don kawai cimma wata manufa ta su.

Cikin mutanen da aka sallama akwai Lieutenant-Colonel Évrard Somda, tsohon shugaban gendarmerie na kasar da Kanal Bamouni Yves Didier, tsohon kwamandan hukumar sirri ta kasar da kwamanda Pousbila Alphonse Zorma, tsohon mai gabatar da ƙara a kotun soji ta birnin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Jigawa ya kori Kwamishina kan zargin lalata da matar aure

Bayanai sun ce mafi yawan sojojin da aka sallama ɗin dama sun daɗe a gidajen yari bisa zarginsu da ƙullawa ƙasar maƙarƙashiya.

Leave a Reply