Mutum 7 sun rasu bayan motarsu ta taka nakiya

0
56
Mutum 7 sun rasu bayan motarsu ta taka nakiya

Mutum 7 sun rasu bayan motarsu ta taka nakiya

Aƙalla masu sare bishiyu bakwai ne suka rasa rayukansu, wasu biyar kuma suka jikkata a jihar Borno a lokacin da motarsu ta taka wata nakiya da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, in ji jami’ai a ranar Litinin.

Bakura Abba, shugaban ‘yan sa kai da ke yaki da ta’addanci a yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa lamarin ya afku da safiyar ranar Asabar a wani yanki mai nisa a Konduga, cibiyar karamar hukumar da ke jihar Borno a arewa maso-gabas.

“Masu sare bishiyoyin na neman itatuwan da za su kona su mayar da su gawayi, abin takaici sai suka taka bam din da aka dasa a gefen hanya, kuma bakwai daga cikin su sun mutu.” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta wayar tarho.

Wasu mutanen biyar kuma sun samu raunuka, inda ake ci gaba da kula da su a asibitin yankin, in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Mutum 11 a Uganda sun mutu bayan fashewar tankar mai

Ba a samu bayanai game da lamarin da wuri ba sakamakon katsewar hanyoyin sadarwa a yankin, wanda ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda sama da shekaru 10, musamman ma ‘yan ta’addan Boko Haram da na ISWAP.

Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ‘yan ta’adda na dasa bama-bamai a kan hanyoyi da kusa da gidaje, da manufar kai hari kan jami’an tsaro, amma sai su kare da kashe fararen hula.

Leave a Reply