Babu ɓaraka ko rashin jituwa tsakanin Abba da Kwankwaso – NNPP

0
30
Babu ɓaraka ko rashin jituwa tsakanin Abba da Kwankwaso - NNPP

Babu ɓaraka ko rashin jituwa tsakanin Abba da Kwankwaso – NNPP

Daga Ibraheem El-Tafseer

Batun rashin jituwa ko ɓaraka tsakanin gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba gaskiya ba ne.

A sanarwa da mai bawa Gwamna Abba shawara na musamman kan kafofin yaɗa labarai na zamani, Salisu Yahaya Hotoro ya fitar, ya ce muna so mu yi ƙarin bayani game da rahoton da Daily Nigerian ta wallafa wanda ke yawo a kafofin sada zumunta na yanar gizo game da wata jita-jitar rashin jituwa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da mai ba shi shawara na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wannan jita-jita ba gaskiya ba ce kuma yaudara ce. Gwamna Abba Yusuf yana da kyakkyawar dangantaka da girmamawa ta gaskiya da aiki tare da Sanata Rabiu Kwankwaso, yana kuma ganin shi a matsayin jagora a tafiyar siyasar sa da kuma a jam’iyya baki daya. Duk wani rahoto da ke cewa akwai sabani tsakanin su, an yi wa gaskiyar lamarin kuskure da yawa.

KU KUMA KARANTA: Da gaske ne an fara samun saɓani tsakanin Kwankwaso da Abba?

Gwamna Abba K. Yusuf ya dukufa wajen ganin an cika manufofi da hangen nesa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Ya himmatu wajen hada kan jam’iyya da aiki tare da dukkan mambobi, ciki har da Kwankwaso, domin cimma burin da muke dasu a cikin gida.

Muna kira ga jama’a da kafofin yada labarai su guji yada labaran da ba a tabbatar da ingancinsu ba, wadanda ka iya kawo matsala ga kokarinmu na hadin kai.

A ƙarshe, Gwamna Abba Yusuf ya mayar da hankali kan manufofin gwamnatinsa kuma yana ci gaba da fifita jin dadin al’ummar Kano.

Muna rokon dukkan mambobin jam’iyya da kafofin yada labarai su goyi bayan hadin kan jam’iyyarmu domin cimma muradun da muka sanya a gaba.

Leave a Reply