Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sakin ƙananan yaran da aka kama lokacin zanga-zanga

0
30
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sakin ƙananan yaran da aka kama lokacin zanga-zanga

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sakin ƙananan yaran da aka kama lokacin zanga-zanga

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni kan a saki ƙananan yaran da aka kama a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a watan Agusta.

Umarnin na shugaban Najeriyar na zuwa ne bayan an gurfanar da yaran a gaban kotu a makon da ya gabata, lamarin da ya jawo zazzafan martani daga ɓangarori daban-daban a faɗin ƙasar.

Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris a ranar Litinin ya shaida wa manema labarai kan cewa Shugaba Tinubun ya bayar da umarnin a gaggauta sakin yaran ba tare da la’akari da duk wata shari’a da suke fuskanta ba.

KU KUMA KARANTA: Dokar ;yancin yara ba ta yarda a gabatar da yara a kotu ba, ballantana hukuncin kisa ; Babban Lauya

Shugaban ya kuma umurci ma’aikatar jin kai da rage radadin talauci da ta gaggauta duba lafiyar wadannan yara ƙanana, sannan kuma ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin sun hadu da iyayensu ko masu kula da su a duk inda suke a ƙasar.

Shugaba Tinubun ya kuma ba da umarnin a kafa wani kwamiti wanda ma’aikatar kula da jin kai za ta jagoranta domin duba duk wasu batutuwan da suka shafi kamawa, tsare su, kulawa da kuma sakin yaran.

Leave a Reply