‘Yansanda sun kama ‘yan ƙasar waje 113, da ake zargi da sata ta yanar gizo

0
28
'Yansanda sun kama 'yan ƙasar waje 113, da ake zargi da sata ta yanar gizo

‘Yansanda sun kama ‘yan ƙasar waje 113, da ake zargi da sata ta yanar gizo

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta kama mutane 130, ciki har da ‘yan ƙasar waje 113, galibinsu ‘yan ƙasar Sin da Malaysiya, da kuma ‘yan Najeriya 17 bisa zargin yin sata ta yanar gizo da wasu ayyukan da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Mutanen sun haɗa da maza 87 ‘yan ƙasar waje da mata 26, tare da maza huɗu da mata 13 ‘yan Najeriya, aka kama su a wani sumamen da aka kai kan wasu ayyukan sata ta yanar gizo.

A cewar ACP Olumuyiwa Adejobi, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, an gudanar da sumamen ne a yau 3 ga Nuwamba, 2024, a wani gini kusa da Next Cash and Carry a Jahi, Abuja.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama tagwaye ’yan yahoo

AIG Benneth Igweh na shiyya ta 7 ne ya jagoranci aikin tare da haɗin gwuiwar cibiyar yaki da laifukan yanar gizo ta ƙasa (NPF-NCCC), inda suka ƙwace kwamfutoci da wasu na’urori masu da ake amfani da su wajen aikata laifin.

Leave a Reply