Dokar ‘yancin yara ba ta yarda a gabatar da yara a kotu ba, ballantana hukuncin kisa – Babban Lauya

0
59
Dokar 'yancin yara ba ta yarda a gabatar da yara a kotu ba, ballantana hukuncin kisa - Babban Lauya

Dokar ‘yancin yara ba ta yarda a gabatar da yara a kotu ba, ballantana hukuncin kisa – Babban Lauya

Mai yuwuwa ne wasu ƙananan yara su 29 su fuskanci hukuncin kisa a Najeriya, bayan da aka gabatar da su a gaban kotu a ranar Juma’a, bisa laifin shiga zanga zangar tsada da matsin rayuwa da aka yi a kasar. Hudu daga cikin su take suka some a kotun, saboda tsananin wahala kafin su kai ga shiga yarjejeniyar amsa laifin su.

Kimanin masu zanga zangar su 76 ne aka tuhuma da manyan laifuffuka 10 da ya hada da cin amanar kasa, lalata kayayyaki, tada hankalin jama’a da bijire ma hukuma, kamar yadda yake kunshe a takardar tuhumar da kafar labarum Associated press tayi tozali da ita.

Kamar yadda takardar tuhumar ta nuna, shekarun yaran ya kama ne daga 14 zuwa 17 kacal da haihuwa.

Bakinciki da takaici kan tsananin tsadar rayuwa a Najeriya ya haifar da zanga zanga iri iri a yan watannin baya a kasar. Akalla an kashe mutane 20 har lahira a watan Agusta, aka kuma garmake daruruwa a yayin wata zanga zanga da matasan kasar suka gudanar, inda suka nemi a sama musu, damarmaki da ya hada da samar musu ayyukan yi.

Tun a cikin shekarun 1970 ne dai aka bullo da hukuncin kisan a Najeriya, to amma ba’a kashe kowa ba a kasar tun shekarar 2016.

Wani lauya mai zaman kan shi dake zaune a Abuja babban birnin kasar, Akintayo Balogun, yace dokar yancin yara ba ta yarda asa yara fuskantar kaikomon shari’ar aikata laifi ba balle har a yanke musu hukuncin kisa. Don haka yace kuskure ne a gabatar da yara a gaban babbar kotun tarayya, sai fa har idan gwamnati ta babbatar cewa yaran sun haura shekaru 19 a duniya.

Lauya Marshal Abubakar dake wakiltar wasu daga cikin yaran yace, kotu ta bayar da belin ko wane daya daga cikin yaran akan kudi dalar Amurka $5, 900 tare da aza musu matakai masu tsananin tsauri, da har yanzu suka gaza cikawa.

KU KUMA KARANTA:Isra’ila ta tagayyara ƙananan yara fiye da dubu 400 a Lebanon – UNICEF

Abubakar ya kara da cewa, kasar da ta gaza ba yaran ta ilmi shine zata zabi ta hukunta wadannan yaran. Yaran dai sun kasance a tsare na tsawon kwanaki 90 ba tare da abinci ba.

Babban shugaban wata kungiyar fafutuka da karfafa shugabanci na gari a Najeriya, Yemi Adamolekun yace, ba abunda ya hada hukumomi da daure yara kanana.

Adamolekun ya kara da cewa, kamata yayi babbar mai shari’a ta Najeriya taji kunyar wannan lamarin a matsayin ta na mace kuma uwa.

Baya ga kasancewa daya daga cikin manyan masu samar da mai a Afrika, Najeriya na cigaba da kasancewa daya daga cikin matalautan kasashe a duniya. Cin hanci da rashawa da yayiwa kasar katutu ya zama abun ado ga jami’an gwamnatin kasar. Kwararru a fannin kiwon lafiya sun rika gudanar da zanga zanga akai akai don nuna rashin jin dadi da rashin gamsuwa kan dan abinda ake biyan su, da bai taka kara ya karya ba.

Leave a Reply