An samu ƙarancin fitowar jama’a, a zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

0
27
An samu ƙarancin fitowar jama’a, a zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

An samu ƙarancin fitowar jama’a, a zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a ranar Asabar a jihar Kano ya gamu da ƙalubalen rashin fitowar jama’a rumfunan zaɓe yayin da jami’an tsaro musamman ‘yansanda ba su fito aikin ba da tsaro ba kamar yadda aka saba gani a lokutan kaɗa ƙuri’a.

Ba a ga fitowar jama’a ba a galibin mazaɓu da rumfunan zaɓe a sassan jihar ta Kano, yayin da wasu wuraren babu labarin kai kayayyakin zaɓe, kuma ƙalilan ne daga cikin cibiyoyin da suka samu kayayyakin zaɓen aka kammala zaɓen da ƙarfe goma zuwa sha ɗaya na rana.

Suma dai jami’an tsaro, musamman ‘yansanda sun kauracewa wuraren kada kuri’a domin bada tsaro, kuma ta yuwu saboda hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano ne, da ya haramta musu halartar cibiyoyin zaben.

Wasu kadan daga cikin mutanen da suka je rumfunan zaben domin kada kuri’a, sunce sunyi amfani da dokar kasa da ta basu damar kada kuri’ar su ga wanda suke so, kuma ‘yan kwamitin tsaro da suka kunshi jami’an tsaron sa kai dana Karota sun bada kariyar tsaro a rumfunan zabe.

KU KUMA KARANTA:Kotu a Kano, ta ba da umarnin a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar

Ana ganin baya ga dambarwar shari’a data dabaibaye sha’anin zaben da yanke kauna ga yin adalci ko sahihanci akan harkar zaben kananan hukumomi a Najeriya, matsin rayuwa a kasa na daga cikin dalilan da suka sa dinbin mutanen jihar Kano suka kauracewa wannan zaben na 26 ga watan na Oktoba.

Manyan jam’iyyun hamayya, PDP da APC ba su shiga zaben ba, amma a cewar shugaban hukumar zaben ta Kano Farfesa Sani Lawan Malumfashi, 6 daga cikin kananan jam’iyyu a Najeriya da suka hada da AA, AAC ACCORD, ADC APM da kuma jam’iyyar NNPP mai gwamnati a jihar Kano, sun shiga zaben.

Kano dai na cikin rukunin karshe na jihohin dake fafutikar samar da zababbun shugabanni a kananan hukumomi da nufin cika umarnin kotun kolin Najeriya, wadda ya haramta nada kantomomi da gwamnoni ke yi su tafiyar da mulkin kananan hukumomi a Najeriya.

Leave a Reply