Faɗuwar tankar mai a Jigawa, mutane 94 sun ƙone ƙurmus, 50 sun samu raunuka

0
37
Faɗuwar tankar mai a Jigawa, mutane 94 sun ƙone ƙurmus, 50 sun samu raunuka

Faɗuwar tankar mai a Jigawa, mutane 94 sun ƙone ƙurmus, 50 sun samu raunuka

Daga Abubakar M Taheer

A ranar Talata da misalin ƙarfe 11:00 na dare, wata Tanka ɗauke da Man Fetur da ta taso daga Kano zuwa Nguru ta faɗi a kusa da Khadija University Majia, da ke jihar Jigawa.

Cikin wata sanarwar gaggawa da jami’an hulɗa da jama’a na hukumar ‘yansanda ta jihar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adam ya fitar, ya bayyana yadda lamarin ya auku.

Bayan faɗuwar Tankar ke da wuya man ya rinƙa kwarara magudan ruwa wanda al’ummar garin suka fito domin kwasar man Fetur ɗin, a nan take wuta ta kama inda nan take mutane 94 suka ƙone ƙurmus. Sauran mutane 50 kuma sun samu munanan raunuka inda aka garzaya da su babban Asibitin Ringim domin a yi musu magani.

Kwamishinan ‘yansanda CP AT Abdullahi ya jajantawa al’ummar Majia dama jihar Jigawa baki ɗaya kan wannan iftila da ya same su tare da addu’ar Allah ya jiƙan Wanda suka rasu.

KU KUMA KARANTA: Wannan gobara ta tankar mai ta yi matuƙar kaɗa mu – Gwamna Fubara

Ya kuma buƙaci al’umma da su rinƙa kulawa sosai da lamarin faɗuwar tankar man fetur wanda take saurin kamawa da wuta bayan faɗuwar ta.

Zuwa haɗa wannan rohoton al’ummar garin na Majia na cikin halin kaɗuwa bisa wannan mummunan ifitila’i daya auka musu.

Leave a Reply