Mahajjata a Kano, za su fara ajiyewa naira miliyan 8 na Hajjin baɗi – Ɗan Bappa

0
41
Mahajjata a Kano, za su fara ajiyewa naira miliyan 8 na Hajjin baɗi - Ɗan Bappa

Mahajjata a Kano, za su fara ajiyewa naira miliyan 8 na Hajjin baɗi – Ɗan Bappa

Hukumar Jin Dadi da Walwalar Alhazai ta jihar Kano ta sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin wani ɓangare na kuɗin aikin Hajjin baɗi da kowanne maniyyaci zai ajiye.

Shugaban hukumar, Alhaji Laminu Rabi’u Ɗanbappa ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da jami’an aikin Hajji na ƙananan hukumomi a Hedikwatar hukumar.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Suleman Dederi ya fitar a jiya Litinin Kano, Danbappa ya ce Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ce ta bada umarnin a sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin kason farko na kuɗin aikin Hajjin 2025.

KU KUMA KARANTA:Hukumar Alhazan Nijeriya ta ƙaryata zargin bai wa mahajjata abinci kaɗan

Ya kuma hori maniyyatan da su tabbatar sun biya kudaden su a kan lokaci.

Hakazalika Danbappa ya sanar da cewa NAHCON ta baiwa Kano kason kujerar alhazai 4,356, wanda a cewar sa, za a rarraba su a kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya kuma sanar da cewa jihar Kano ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin na baɗi, inda ya yi fatan a yi shi cikin nasara.

Leave a Reply