Kotu a Kaduna ta hana wani mutum shiga ɗakin tsohuwar matarsa

0
43
Kotu a Kaduna ta hana wani mutum shiga ɗakin tsohuwar matarsa

Kotu a Kaduna ta hana wani mutum shiga ɗakin tsohuwar matarsa

Wata kotun shari’a da ke zaune a Magajin Gari, Kaduna, Jihar Kaduna, ta umarci wani mutum, Aminu Adamu, da ka da ya ziyarci ɗakin tsohuwar matarsa domin ganawa da ‘ya’yansa.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), alƙalin kotun, Malam Anas Khalifa, ya yanke hukuncin ne bayan tabbatar da saki uku da Aminu ya yi wa tsohuwar matarsa, Jamila Sani.

“Babu aure a tsakaninku saboda furucin saki da ka yi. Dole ka kaucewa haduwa da ita a sirrance.

“Idan ka na bukatar ganin ‘ya’yanka, ka gan su a wajen dakinta,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA:Wata kotu ta tsare magidanci kan yi wa ’yarsa fyaɗe

Alkalin ya kuma umarci Aminu da ya ci gaba da daukar nauyin abincin ‘ya’yansa, kudin makaranta, wurin zama da lafiyarsu.

Tun da farko, mai kara, Jamila ta roki kotu da ta tabbatar da furucin saki na uku da Aminu ya yi a watan Yuni kuma ta ba ta ikon riƙe ‘ya’yanta.

Aminu ya kuma yi alkawarin ba tsohuwar matarsa N15,000 duk mako a matsayin kudin ciyarwar ‘ya’yansu.

Leave a Reply