Zaluncin Isra’ila ne ya haifar da faɗa tsakanin su da Hamas – Dakta Elharoun Muhammad

0
65
Zaluncin Isra'ila ne ya haifar da faɗa tsakanin su da Hamas - Dakta Elharoun Muhammad
Dr. Elharoun Muhammad

Zaluncin Isra’ila ne ya haifar da faɗa tsakanin su da Hamas – Dakta Elharoun Muhammad

Dakta Elharoun Muhammad a hirarsa da sashen Hausa na Rediyo Faransa, ya bayyana cewa zaluncin Isra’ila ne ya haifar da faɗa tsakanin su da Hamas, Hizbullah da jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A tattaunawar ta su, ya bayyana cewa “wannan yaƙi da yake gudana, wanda yake ƙara haɓaka a ɗan tsakanin nan, yana nema ya haɗa ƙasashen Larabawa da ma waɗanda ba larabawa ba, yana da nasaba da gazawar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi.

Yana da nasaba da gazawar da ƙungiyar Larabawa ta yi. Yana da nasaba da zaluncin da Yahudun Isra’ila suke yi. Shi ya sa duk abubuwan suka damalmale, ana kallo ana zalunci aka ka sa ɗaukar matakin da ya kamata.

Gazawar Majalisar Ɗinkin Duniya shi ya haifar da zuwa yanzu an kashe mutane sama da dubu 45. Jagororin gazawar Majalisar Ɗinkin Duniya, sune, ƙasar Amurka da ƙasashe biyar da suka haɗu suka yi security council, waɗanda suke da ƙarfin hawa kujerar na ƙi. Su suka ɗaure wa Yahudun Isra’ila gindi, suke irin waɗannan abubuwan.

Akwai ƙuduri na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda dokar duniya ta tanadi cewa, Larabawan nan suna da haƙƙi a wannan waje. Yau sama da shekaru 70, ana wannan zaluncin na kisan gilla, kuma akwai dokoki ga wanda ya yi kisan gillar, amma an gaza. Ka ga wannan ƙalubale ga Dimokuraɗiyya, ‘Yan rajin kare haƙƙin ɗan’adam da Majalisar Ɗinkin Duniya”.

TAMBAYA: Kenan waɗannan ƙasashe guda 5, idan ba su so ba, babu abin da zai tafi daidai a duniya?

DAKTA ELHAROUN: Ai daman duniyar ta suce. Su suka zauna suka tsara, China, Rasha, England, Amurka duk abu ɗaya ne. Saboda haka su suka haɗu, suka yi yaƙin duniya na ɗaya, su suka yi na biyu. Bayan sun yi mulkin mallaka, suka kafa Majalisar Ɗinkin Duniya, suka fifita kansu a kan ƙasashe 194.

TAMBAYA: Me za ka ce game da shirin Isra’ila na kai hari a ƙasar Iran, kana ga wannan yaƙi zai ƙare kwana kusa kuwa?

KU KUMA KARANTA: Mun shirya mayar da martani kan duk harin da aka kawo mana – Iran

DAKTA ELHAROUN: Ai wannan yaƙin ina ga shi zai kawo ƙarshen duniya gabaɗaya, saboda zaluncin ya kai zalunci. Kuma Iran a shirye take duk abin da za a yi, a yi kawai. Su suna ga farilla ne Allah ya ɗora musu su yaƙi zalunci da danniya, wanda Isra’ila ta ɗaurewa gindi.

Saboda haka babu mamaki Isra’ila ta rama wannan hari da Iran ta kai musu. Kuma Iran a shirye take saboda ta gargaɗi ƙasashen Larabawa. Ta ce duk ƙasar da ta yi kuskuren ba da wuri a Amurka ko Yahudun Isra’ila suka kawo musu hari, to za su yaƙi wannan ƙasar. To ai ka ga kawai za a ce yaƙin duniya ya fara.

TAMBAYA: Netanyahu ya ce sai ya canza taswirar gabas ta tsakiya, me za ka ce kan haka?

DAKTA ELHAROUN: Ai daman yana daga cikin manufarsu, su gama da Falasɗinu, Lebanon, Jordan, Misira da Siriya. Sun ce Makka da Madina ma garin kakanninsu ne, sun ce sai sun je nan ma, ka ga wannan ai duniya suke so su ƙwace.

Leave a Reply