‘Yan bindiga a Kebbi sun kashe mutum 1, sun sace Basarake

0
27
'Yan bindiga a Kebbi sun kashe mutum 1, sun sace Basarake

‘Yan bindiga a Kebbi sun kashe mutum 1, sun sace Basarake

Daga Umar Idris, Zariya

An tabbatar da wani mummunan hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya, uku suka jikkata, sannan sun yi awon gaba da wasu mutane takwas, ciki har da basaraken garin, Alhaji Isah Daya.

An kai harin ne da tsakar dare a ranar Asabar . Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne inda suka kashe Sherrif Alhaji Almu, tare da jikkata wasu mutane uku da ke kwance a asibiti a halin yanzu. Bugu da kari, an yi garkuwa da mutane takwas da suka hada da basaraken gundumar Garin na Kanya, Alhaji Isah Daya.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kebbi, SP Nafui Abubakar, ya tabbatar da faruwar harin. Ya bayyana cewa, rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin ‘yansanda ta kaddamar da farautar mutanen da aka sace tare da tabbatar da cewa ta cafke waɗanda suka aikata laifin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a Haiti

“Gwamnatin jihar Kebbi ta samar da kayan aikin da suka dace don yakar ‘yan bindiga a yankunan da abin ya shafa, musamman masarautar Zuru,” in ji SP Nafi’u Abubakar.

Wannan lamari dai ya biyo bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai a karamar hukumar Suru, inda aka kashe shugaban jam’iyyar APC, tare da yin garkuwa da mutum daya a kauyen Matseri da ke karamar hukumar Bunza a cikin makon da ya gabata.

Leave a Reply