Ranar Malamai Ta Duniya: Malaman Nijar sun koka kan halin da suke ciki

0
91
Ranar Malamai Ta Duniya: Malaman Nijar sun koka kan halin da suke ciki

Ranar Malamai Ta Duniya: Malaman Nijar sun koka kan halin da suke ciki

An gudanar da bikin Ranar Malaman Makaranta ta Duniya na bana (2024), wanda majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a shekarar 1994 da nufin ƙarfafa wa malamai guiwa a ayyukan ilmantar da al’umma.

A bana ranar ta zagayo a wani lokacin da malaman makaranta a jamhuriyar Nijar ke fama da tarin matsaloli masu nasaba da yanayin rayuwa, da na aiki yayinda wasu yankunan kasar ke fuskantar matsalolin tsaro masu tada kayar baya wadanda ke yi wa malamai barazana.

Ranar malamai ta duniya da ke matsayin wani lokacin bitar halin da malaman makaranta ke gudanar da ayyuka na zama wata damar jin ta bakinsu a game da yanayin rayuwar da suke ciki don magance wa da kuma inganta abinda ke bukatar gyara.

Taken ranar ta bana shine a bai wa muryoyin malamai mahimmanci sai dai Karancin albashi da rashin samunsa akan lokaci na daya daga cikin matsalolin da ke addabar malamai a yanzu haka a Nijar.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Matsalolin tsaron da ake fama da su a wasu yankunan kasar abu ne da ya haddasa koma bayan sha’anin ilimi a ‘yan shekarun nan duk da matakan da hukumomi ke dauka a ayyukan karantarwa.

Malan Cherif Issoufou sakataren kungiyar malamai ta SYNACEB ta Nijer yace, malaman makaruntu suna fuskantar kalubale mussamma a ta bangaren Rashin tsaro.

Sama da kashi 80% na malaman makaranta ‘yan kwantaragi ne, a baya gwamnatin kasar ta yi alkawalin shigar da wani rukuni na malaman a sahun ma’aikatan dindindin da nufin inganta sha’anin ilimin boko sai dai shiru kake ji dalili kenan da gamayyar kungiyoyin malamai ta Dynamique ta shiga yunkurin tada hukumomi daga barci a taron manema labarai, karon farko kenan bayan juyin mulkin a kasar.

Malan Laouali Issoufou magatakardan kungiyar malamai ta SNEN yace, ya kamata a gyara Albashi malamai kuma a dinga biyan su akan lokaci.

A ranar 28 ga watan Octoban ne ya kamata a koma makaranta bayan kammala babban hutu. Gamayyar Dynamique na gargadin gwamnati ta yi amfani da dan lokacin da ya rage don warware dukkan wasu matsaloli da malamai ke fuskanta.

A wata wasikar da ma’aikatar kwadago ta kasa ta aike wa kungiyoyin kwadago a ranar alhamis din da ta gabata, sun bukaci jagororin ma’aikata su hallara a taron tantaunawar da za a yi a makon gobe da kwamitin ministoci mai alhakin sulhunta bangaren gwamnati da na ma’aikata.

Leave a Reply