Najeriya ta fara shirin kwaso ‘yan ƙasarta daga Lebanon

0
26
Najeriya ta fara shirin kwaso 'yan ƙasarta daga Lebanon

Najeriya ta fara shirin kwaso ‘yan ƙasarta daga Lebanon

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara shirin kwaso mutanen da ke zama a ƙasar Lebanon, biyo bayan ta’azzarar rikici tsakanin Isra’ila da Iran.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman akan al’amuran kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun ne ya bayyana haka a ranar Talata sannan ya bukaci ‘yan Najeriya mazauna Lebann su tuntubi ofishin jakadancin don su ba da bayanan su.

A wani sakon da ya kafa a adireshin shafinsa na X @DOlusegun, mai bai wa shugaban shawara ya ja hankalin duk ‘yan Najeriya da ke Lebanon da “su tuntuɓi ofisihin jakadancin ƙasar don ba da bayanansu gabanin a fara kwashe su”.

A ranar Talata, Iran ta harba makamai masu linzami 180 cikin Isra’ila a matsayin martini akan kisan shugabanin Hezbollah.

KU KUMA KARANTA: Israila ta kashe shugaban Hizbullah na Lebanon

Ƙasashen 2 sun yi ta barazana tsakanin su bayan ruwan makamai masu linzamin da Tehran tayi.

Firan ministan Isra’ila Beyamin Netanyahu, ya lashi takobi cewa, Isra’ila zata mai da martini mai zafi akan harin da aka kai mata.

A nasu bangaren kuma, kasar China da Saudi Arabiya sun yi ƙira da a kwantar da wannan tarzomar da take dada ruruwa a yankin Gabas ta tsakiya sannan, sun yi ƙira ga ɓangarorin biyu da su dawo kan teburin tattaunawa.

Leave a Reply