Mutane 2 sun mutu a Ibadan a wani ambaliyar ruwa

0
2626
Mutane 2 sun mutu a Ibadan a wani ambaliyar ruwa

Mutane 2 sun mutu a Ibadan a wani ambaliyar ruwa

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da rasuwar mutane biyu a yayin da wasu biyu suka bace a sanadiyyar wani ruwan sama da aka yi a ranar Talata wanda ya haifar da ambaliya a sassan birnin Ibadan, fadar jihar Oyo.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kodineto na Hukumar NEMA shiyyar Kudu maso Yamma, Olanrewaju Kadiri, ya ce ambaliyar ruwan ta yi sanadin rushewar wasu gidaje da shaguna da ƙadarori na miliyoyin kuɗi.

Ya ce yanzu haka hukumar da haɗin kan SEMA ta Jihar Oyo da ƙungiyar Red Cross suna kan aikin ziyarar unguwannin da lamarin ya shafa domin ƙididdige irin ɓarnar da ambaliyar ta haifar.

Ambaliyar ta shafi yankin ƙaramar hukumar Ibadan ta Yamma ne inda al’amuran yau da kullum suka tsaya cik na tsawon awoyi biyar da aka yi ana yin ruwan saman kamar da bakin ƙwarya.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar Ruwa: Gidauniyar tunawa da Sardauna ta ba da tallafin naira miliyan 20 a Maiduguri

Binciken ya nuna cewa matakin hana zuba shara a magudanun ruwa da suka kewaye birnin Ibadan da gwamnatin jihar ta dauka tun kafin isowar wannan lokaci ya taimaka wajen samun saukin ambaliyar.

Leave a Reply