Ƙarin farashin man fetur ya karya darajar mafi ƙarancin albashi na dubu 70 — NLC

0
13
Ƙarin farashin man fetur ya karya darajar mafi ƙarancin albashi na dubu 70 — NLC

Ƙarin farashin man fetur ya karya darajar mafi ƙarancin albashi na dubu 70 — NLC

Ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC) a ranar Alhamis ta ce za ta gana da gwamnatin tarayya kan yadda ma’aikata za su tsira daga ƙarin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan.

A cewar ƙungiyar ƙwadago, farashin man fetur a halin yanzu ya durƙusar da nasarorin da ake zaton an samu a kan sabon tsarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata na N70,000 da har yanzu ba a fara aiwatar da shi ba, in ji shugaban NLC, Joe Ajaero.

KU KUMA KARANTA:Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu – NLC

Ya bayyana hakan ne a wajen bukin bude taron karawa juna sani na yini biyu kan aiwatar da mafi karancin albashi na shiyyar Kudu a Legas.

Ya nanata cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne ya yaudari kungiyar kwadago ta karbar mafi karancin albashi na N70,000 saboda ba zai yi karin farashin man fetur ba.

Ya shawarci gwamnati da ta magance matsananciyar yunwa da fatara da bacin rai da ‘yan Najeriya ke fama da su kafin al’amura su kazance, yana mai korafin cewa lallai ‘yan Najeriya na cikin wahala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here