Ba mu gama tantance adadin waɗanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwa a Maiduguri ba – NEMA
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta bayyana cewa har yanzu ba a kai ga tantance yawan rayukan da aka yi asara ba, a dalilin ambaliyar ruwan da ta faru a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Tun bayan bayyanar adadin mutane 30 da suka mutu da hukumar ta NEMA ta sanar, sanadin ambaliyar ruwan da aka yi a Maiduguri, daga bisani hukumar ta bayyana cewa, a yanzu ba ta da takamaiman adadin wadanda suka rasa rayukansu, saboda har yanzu ruwa bai janye daga unguwanni da dama da ruwan ya cinye ba.
Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, Malam Sirajo Abdallah ne ya bayyana hakan, inda ya ce baya ga mamaye unguwanni da ruwan yayi, akwai sauran wurare kamar makabartu da sauransu da ruwan ya mamaye.
Ya kuma ce dole ne sai idan ruwan ya janye sannan a iya tantancewa a kuma gano irin barnar da ruwan yayi, kuma za a gudanar da tantancewar tare da shugabannin al’umma a, unguwanni dabam dabam da ruwan ya ci.
KU KUMA KARANTA:Ambaliyar ruwa a Arewa ta kashe mutum 49, ta raba 41,344 da muhalli – NEMA
Ambaliyar ruwan ta Maiduguri dai ta raba mutane da dama da matsugunnansu, inda gidaje da dama suka rushe, wasu kuma ruwa ya shafe su baki daya.
A yanzu dai gwamnatin jihar Borno ta tsugunnar da dubban mutanen da ambaliyar ta raba da gidajensu a sansanonin ‘yan gudun hijira, sai dai mutane da dama sun koka da rashin abinci da wajen kwanciya, inda suka bayyana cewa a wasu lokutan ana dukansu akan layin karbar abinci, ba babba ba yaro, lamarin da suka ce ya kai ga rasa rai, wasu kuma na kwance a asibiti sakamakon kuna da su ka samu a wurin karbar abinci.
Hukumomi da masu hannu da shuni cikin al’umma, manya da kananan ‘yan kasuwa a Najeriya na ci gaba da aikewa da gudummuwa domin tallafa wa al’ummar ta Maiduguri da ambaliyar ruwan ta shafa.