Da wane dalili PDP ta dakatar da Dino Melaye?

0
0

Da wane dalili PDP ta dakatar da Dino Melaye?

Jam’iyyar PDP ta dakatar da Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi kan wasu zarge-zarge na yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.

Wannan mataki, a cewar wata takarda da jaridar TRIBUNE ONLINE ta gani a yau Juma’a, kwamitin gudanarwar jam’iyyar na gundumar Ayetoro/Iluagba Ward 1 ya yanke shi ne bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa domin bincikar laifukan da Melaye ya aikata.

KU KUMA KARANTA:Yadda Melaye, da wasu ‘yan jam’iyya suka fice daga cibiyar tattara sakamakon zaɓe a fusace

Ga dukkan alamu abubuwan da Melaye ya yi a baya-bayan nan sun saɓa wa manufofin jam’iyyar PDP da haɗin kai, wanda ya sa aka dakatar da shi.

Leave a Reply