Gwamnatin Kano ta ɗaga ranar komawa hutun makarantun firamare da sakandare

0
138
Gwamnatin Kano ta ɗaga ranar komawa hutun makarantun firamare da sakandare

Gwamnatin Kano ta ɗaga ranar komawa hutun makarantun firamare da sakandare

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ɗage lokacin komawa makarantun Firamare da Sakandare domin fara zangon Karatu na 2024 zuwa 2025.

Daraktan hulɗa da jama’a da wayar da kan al’umma na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Ƙiru cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ambato Kwamishinan ilimi Umar Haruna Doguwa na cewa daukar matakin ya Zama dole saboda wasu dalilai.

Umar Doguwa ya ce nan gaba kadan gwamnati zata sanar da lokacin komawar a hukumance.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

“Ina son shaidawa dalibai da Iyayen yara cewa an sauya lokacin komawa makaranta wanda aka tsara za’a koma a ranakun 8 da 9 ga watan satumbar 2024, hakan ya faru ne saboda wasu dalilai, muna kokarin ganin an samu yanayi mai kyau na koyo da koyarwa a makarantu, Nan gaba kadan za mu sanar da lokacin komawar,” inji Kwamishinan.

Sanarwar ta buƙaci ɗalibai da Iyayen yara da su yi hakuri kan tsaikon da aka samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here