Ba a biyan harajin da ya dace a Najeriya – Bill Gates

0
96
Ba a biyan harajin da ya dace a Najeriya - Bill Gates

Ba a biyan harajin da ya dace a Najeriya – Bill Gates

Ɗaya daga cikin hamshaƙan masu kuɗin duniya, Bill Gates, ya ce ba a biyan haraji sosai a Najeriya, kuma hakan yana jawo manyan ƙalubale ga fannonin lafiya da na ilimi a ƙasar.

Bill Gates ya faɗi hakan ne a wajen wani taron tattaunawa da ya yi da matasa a Abuja a ƙarƙashin wani shiri na abinci mai gina jiki wato Nutrivision 2024, a ranar Laraba.

Hamshaƙin attajirin ya faɗi haka ne a lokacin da yake amsa wata tambaya da wata matashiya ta yi masa kan dabarun da Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta iya bi wajen shawo kan manyan matsalolin da ke dabaibaye da fannin lafiya.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da damar shigar da shinkafa, masara, alkama da wake na tsawon wata 5 ba tare da haraji ba

“A tsawon lokaci, akwai shirye-shirye ga Najeriya da za ta saka kuɗaɗe a harkar gwamnati fiye da yadda take yi a yau. Babbar matsalar da ake da ita a ƙasar ita ce ba a biyan haraji sosai,” in ji shi.

Masana tattalin arziki da dama a Najeriya sun sha cewa tsarin biyan haraji na ƙasar na fuskantar matsaloli da dama kamar cin hanci da rashin shugabanci nagari da rashin tsari da rashin adana bayanai da sauran su.

Mista Gates ya ƙara da cewa ‘yan ƙasa da ke son ilimi da lafiya za su iya ƙara jajircewa a fannonin shirye-shiryen gwamnati ko na hukumomi masu zaman kansu.

“Gidauniyarmu suna taka rawa sosai da misalai da dama, inda muke nuna hanya ta yadda za a tabbatar da cewa ana kashe kuɗaɗe yadda ya kamata, ana tafiyar da cibiyoyin lafiya da kyau inda ma’aikata za su yi aiki tuƙuru.”

Kazalika Bill Gates ya ce Najeriya tana da burin zama mai fitar da abinci zuwa ƙasashen waje idan aka yi la’akari da irin ƙasar noma mai faɗi da yalwa da ake da ita.

Leave a Reply