An yi jana’izar mai martaba sarkin Ningi
Daga Ibraheem El-Tafseer
A yammacin ranar Lahadi ne aka yi jana’izar mai martaba sarkin Ningi da ke jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad Ɗanyaya.
Ɗaruruwan jama’a ne suka halarci jana’izar ta sa wadda aka gudanar da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin yau Lahadi a fadarsa da ke cikin garin Ningi.
Cikin waɗanda suka halarci jana’izar har da Gwamnan Bauchi, Alhaji Bala Abdulƙadir Mohammed da dukkan sarakunan jihar Bauchi, da wasu daga cikin sarakunan Yobe da Gombe.
KU KUMA KARANTA:Mai martaba sarkin Ningi ya rasu
Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu, yana da shekara 88.