Kisan Sarkin Gobir: Babu hannun mu a ciki — Miyetti Allah

0
75
Kisan Sarkin Gobir: Babu hannun mu a ciki — Miyetti Allah

Kisan Sarkin Gobir: Babu hannun mu a ciki — Miyetti Allah

Ƙungiyar Miyetti Allah ta Ƙasa (MACBAN), ta nisanta kanta da kisan da ‘yan ta’adda su ka yi wa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa a jihar Sakkwato.

Sakataren MACBAN na ƙasa, Bello Aliyu-Gotomo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar a Abuja.

Ya ce ƙungiyar ba ta da hannu a kisan basaraken kuma ita ba ta goyon bayan ta’addanci.

“MACBAN ta nisanta kan ta daga wannan ta’addanci da aka aikata da kuma duk wani nau’i na ta’addanci da kowace ƙungiya ta aikata domin ba ita goyon bayan laifi ko masu laifi,” in ji Sakataren.

Ya ce MACBAN ta yi Allah wadai da garkuwa da mutane da azabtarwa da kuma kisan gilla da aka yi wa Sarkin Gobir.

Aliyu-Gotomo ya ce kisan da aka yi wa basaraken ba wai kawai ya tayar da hankalin jama’a ba ne, illa dai yana nuni da irin ta’addancin wadanda suka aikata laifin.

A cewarsa, babu hujjar ayyukan wadannan kungiyoyin masu kisan kai.

KU KUMA KARANTA:Mutuwar Sarkin Gobir: Mun miƙa komai ga Allah – Iyalansa

“MACBAN tana ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Sakkwato, Sarkin Musulmi, da iyalan Sarkin da aka kashe da kuma daukacin al’ummar Jihar baki daya.

“A madadin daukacin membobinmu da ke fadin kasar nan, muna addu’ar Allah ya jikan Sarkin Gobir ya kuma ba shi lafiya, ya kuma sa Aljannar Firdausi ta zama masaukinsa na karshe.

“Allah Ta’ala Ya baiwa iyalai karfin gwiwar jure wannan babban rashi.

“Muna addu’a da fatan za a tona asirin wadanda suka aikata laifin nan take kuma a yi musu hukunci mai tsauri.”

Leave a Reply