Mai martaba sarkin Ningi ya rasu

0
0

Mai martaba sarkin Ningi ya rasu

Mai Martaba Sarkin Ningi, Dakta Yunusa Muhammadu Ɗan Yaya OON, ya riga mu gidan gaskiya.

Neptune Prime Hausa ta samu labarin rasuwar Sarkin ne a safiyar yau Lahadin a Jihar Kano.

Sarkin ya rasu ne a Asibitin Expert Alliance da ke Kano, kwanaki biyu bayan dawowa daga tafiyar ganin likita da ya je birnin Makkah na Saudiyya.

KU KUMA KARANTA:Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Issa Hayatou, ya rasu

Wata sanarwar da Sakataren Fadar Ningi, Alhaji Usman Sule Magayaƙin Ningi, ta ce za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4.00 na Yamma a fadarsa.

Leave a Reply