Wa ke da hannu a kashe Sarkin Gobir? (Bidiyo)

0
152
Wa ke da hannu a kashe Sarkin Gobir? (Bidiyo)

Wa ke da hannu a kashe Sarkin Gobir? (Bidiyo)

Daga Idris Umar, Zariya

Ɗan Sarkin Gobir na Sabon Birni ya ce Hon. Aminu Boza shi ne wanda ya ba da kwangilar a kashe Sarkin Gobir na Sabon Birni inji Kabiru, shi Kabir ɗane ga Mai Martaba Sarkin Gobir na Sabon Birni kuma jika ga Sarkin Gobir na madawa da ke Jamhuriyar Nijar.

Kabiru wanda ya bayyana hakan a wani gajeren faifan bidiyo mai tsawon sakanni 25 ya ce, ‘yan ta’adda sune suka ce an ba su kwangila ne ta hannun Hon. Boza ɗan Majalisar Jaha a Majalisar dokoki ta jihar Sakkwato wanda ya ke wakiltar yankin Sabon Birni.

Boza ɗan Majalisar jiha ne a ƙarkashin jam’iyyar APC kuma shi ne ɗan Majalisa Mai waƙiltar Yankin na Sabon Birni a Majalisar dokoki ta jihar Sakkwato, inda ya ba da kwangilar akan kuɗi har naira miliyan biyar.

Hon. Aminu Boza

 

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir, Isa Bawa 

‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da Mai Martaba Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Muhammad Bawa, akan hanyar su ta dawowa gida bayan sun kammala taro a gidan Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III.

Sarkin Gobir, Muhammad Bawa, ya shafe sama da sati uku dashi da ɗansa kuma suka ci gaba da gana musu baƙar azaba, inda suka nemi da a ba su kuɗin fansa har naira miliyan sittin da kuma babura guda biyar.

Inda daga bisani suka kashe Sarkin Gobir duk da sun karɓi kuɗi amma Sun hana gawar shi ayimasa Sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Yanzu dai haka sun saki Kabiru wanda yanzu haka yana asibiti yana samun kulawar likitoci.

Bisa wannan zargi ne jama’a ke tambayar ina gaskiyar maganar take ne?

Muna addu’ar ubangiji ya karɓi shahadar Mai Martaba Sarkin Gobir Muhammadu Bawa, Ya sa Aljanna makoma a wajan shi. Allah ya ba wa ‘yan’uwansa da danginsa haƙurin jure wannan babban rashi da aka yi. Ameen.

Kalli bidiyon a nan:

Leave a Reply