Mun gano haramtattun hanyoyin da ake satar man fetur a Najeriya – NNPC

0
96
Mun gano haramtattun hanyoyin da ake satar man fetur a Najeriya - NNPC

Mun gano haramtattun hanyoyin da ake satar man fetur a Najeriya – NNPC

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, ya ce ya gano ƙarin wasu hanyoyi da ake satar ɗanyen man fetur a ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a shafukan sada zumunta, NNPC ya ce, ya gano wasu hayoyin bututan mai 33 da haramtattun matatun man fetur 220.

“Cikin mako guda mun gano haramtattun hanyoyi 33 na bututun mai da haramtattun matatun man fetur 220.” Sanarwar mai taken ‘Yaƙi da satar ɗanyen man fetur’ ta ce.

Wannan sanarwa da kamfanin na NNPC ya fitar na zuwa kwana guda bayan da ya ayyana samun ribar naira tiriliyan 3.3 a shekarar 2023.

KU KUMA KARANTA: Gayawa ‘yan Najeriya gaskiya gamaida tallafin man fetur – Bode George

Kazalika lamarin na faruwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan batun tallafin man fetur da gwamnati Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta cire a bara, amma kuma wasu rahotanni ke zargin ana ci gaba da biyan kudin ta bayan fage.

Shi dai kamfanin na NNPC ya ce kuɗaɗen da ake iƙirarin an biya ba na tallafin mai ba ne duk da rahoton da jaridar yanar gizo ta The Cable ta ruwaito da ke cewa Tinubu ya ba kamfanin na NNPC umarnin ya biya wasu kuɗaɗe a matsayin na tallafin man fetur.

A lokacin haɗa wannan rahoto, ana kuma fama da matsalar ƙarancin man na fetur inda ake ganin dogayen layukan motoci a gidajen mai a manyan biranen ƙasar.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a ranar Litinin ya yi ƙira ga gwamnatin Tinubu da ta fito ta fayyace wa ‘yan Najeriya taƙaddamar biyan kudin na tallafin mai yana mai cewa lamarin ya jefa al’umar ƙasar cikin ruɗani.

Leave a Reply