Rundunar sojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai a Neja-Delta

0
114
Rundunar sojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai a Neja-Delta

Rundunar sojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai a Neja-Delta

Daga Ali Sanni Larabawa

Dakarun sojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun man fetur guda 27 a yankin Neja-Delta da ke kudancin Najeriya, yayin da suka daƙile satar ɗanyan mai da ake yi a yankin.

Rundunar sojin ta kuma ƙwace ɗanyan mai da yawansa ya kai lita 100,000 a yankin na Neja-Delta.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Jonah Danjuma a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, tawagar sojin ta yi aiki tare da binciko inda ake aikata wannan ta’asa tare da samun gagarumar nasara.

Girman matsalar satar ɗanyan mai a Najeriya da ke matsayin ƙasa mafi fitar da ɗanyan mai ya kawo naƙasu ga adadin man da ƙasar ke fitarwa a ƴan shekarun baya-bayan nan.

KU KUMA KARANTA:Najeriya ta gano ‘haramtattun’ matatun man fetur 50 a yankin Neja Delta

Matsalar satar ɗanyan mai ta sanya gwamnatin ƙasar samun koma-baya a wurin samun kuɗin shiga abin da ya zame wa gwamnatin shugaban ƙasar Bola Tinubu babban ƙalubale.

Bayan lalata matatun mai da aka samar ba bisa ƙa’ida ba guda 27 da ƙwace ɗanyan mai da aka sata lita dubu 100, rundunar sojin ta lalata wasu ƙarin matatu 4.

Rundunar sojin ta Najeriya ta buƙaci al’ummar da ke rayuwa a yankunan da ake da albarkatun man fetur da su taimaka mata da bayanan sirri domin daƙile ɓarayin danyan mai dake kassara tattalin arzikin Najeriya

Leave a Reply