Masu zanga-zanga a Kenya na ci gaba da ƙira ga Shugaba Ruto da ya yi murabus

0
65
Masu zanga-zanga a Kenya na ci gaba da ƙira ga Shugaba Ruto da ya yi murabus

Masu zanga-zanga a Kenya na ci gaba da ƙira ga Shugaba Ruto da ya yi murabus

Masu zanga-zanga na cigaba da zanga-zangarsu a Kenya, inda masu fafutuka ne suka shirya zanga-zangar a birnin Nairobi bayan da shugaba William Ruto ya kori kusan dukkanin ministocinsa tare da ƙara ‘yan adawa a cikin abin da ya kira gwamnati mai cikakken tsari.

An rufe harkokin kasuwanci a birnin kuma motocin sufurin jama’a sun kasance daga tsakiyar yankin kasuwanci inda suka saba.

‘Yan sanda sun kuma sanya shingaye a kan hanyoyin shiga birnin, da jefa barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar neman shugaban ƙasar ya yi murabus a babban birnin Kenya a ranar Alhamis yayin da aka rantsar da sabuwar majalisar ministocin kasar.

Ofishin shugaban ƙasar, inda aka rantsar da sabbin ministocin a safiyar ranar Alhamis, shi ma dai an killace shi.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga masu ɗaga tutar ƙasar Rasha

Manyan garuruwa ciki har da birnin Kisumu da ke gefen tafkin, tungar ‘yan adawa da a baya aka gudanar da zanga-zangar ya kasance cikin kwanciyar hankali inda wasu mazauna yankin suka shaida wa manema labarai cewa ba sa zanga-zangar ne saboda an shigar da ‘yan adawa cikin sabuwar majalisar ministocin ƙasar.

Ƙungiyoyin fararen hula, tare da ƙungiyar lauyoyin Kenya, sun yi ƙira a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa don tabbatar da hakkin ɗanAdam a yayin zanga-zangar tare da yin ƙira ga ‘yan sanda da su guji tura ‘yan sandan da ba su da bayanan sirri da kuma amfani da motocin da ba a sani ba.

Leave a Reply